Gidajen Raya Al’adu A Lagos

Sauti 10:05
Umar Garba Duya  da ake kira Susu  a Tube ba riga tare da Wasu 'yan wasan Dandali a freedom Thearter Lagos Nigeria
Umar Garba Duya da ake kira Susu a Tube ba riga tare da Wasu 'yan wasan Dandali a freedom Thearter Lagos Nigeria RFI Hausa/Salisu

Wasannin Dandalin ko na kwaikwayo, wata al’ada ce da aka dade al’ummomin kasashen Africa ke gudanarwa, domin nishadantar da juna, da kuma koyar da al’adu tare da tunatar dasu a lokacin da suke kokarin shudewa.Akan haka Shirin al’adu ya duba yaduwar gidajen Wasannin Kwaikwayo na yan arewa a yankin kudu maso yammacin Nigeria, musamman a garin Lagos tsohon babban birnin Tarayyar Kasar.