Al'adun Gargajiya

Rasuwar Sarkin Kano Ado Bayero

Sauti 10:03
Marigayi Sarkin Kano Ado Bayero
Marigayi Sarkin Kano Ado Bayero nairaland.com

Shirin al'adunmu na gado na wannan Makon ya duba rasuwar Marigayi tsohon Sarkin Kano Dr. Ado Bayero ne da Alla ya yiwa cikawa a ranar Jumu'a 6 ga Watan Yuni. Haka kuma shirin ya duba zaben sabon Sarkin Kanon da aka yi a ranar Lahadi 8 ga Watan na Yunin 2014 kamar yanda za ku ji a cikin shirin al'adunmu na gado da Faruk Muhammad Yabo ke gabatarwa a kowane Mako.