Ali Kwara zai rage masu dauke da makami a Najeriya

Sauti 10:12
Alhaji Ali Kwara
Alhaji Ali Kwara

Shirin al'addunmu na gado na wannan makon tare da Garba Aliyu Zaria ya zanta ne da Alhaji Ali Kwara da ya shahara wajen kama manyan 'yan fashi musamman a arewacin Najeriya. Ali Kwara ya koka kan yadda makamai suka yalwata a hannun miyagun mutane da ke aikata munanan ayyuka a kasar, yayin da ya lashi takobin daukan matakin kakkabe irin wadannan mutanen.