Al'adun Gargajiya

Muhimmancin al'adar tsagen fuska a Nijar

Sauti 10:36
Al'adar tsagen fuska ta ban-banta tsakanin kabilu daban daban a Afrika
Al'adar tsagen fuska ta ban-banta tsakanin kabilu daban daban a Afrika kwaranews.com

Shirin Al'adun Gargajiya na wannan makon tare da Salissou Hamissou ya yi nazari kan muhimmancin al'adar tsage a fuskokin kabilu da dama a Jamhuriyar Nijar. A yayin da wasu ke ci gaba da mutunta wannan al'ada, wasu kuwa na kokarin neman hanyar bankwana da ita saboda yadda ake ci gaba da samun wayewa a sassa daban-daban na duniya.