Pakistan

Pakistan da Afghanistan rikici da yan Taliban

Shugaban kasar Pakistan Asif Ali Zardari.
Shugaban kasar Pakistan Asif Ali Zardari. Wikimedia / Eric Draper

Kasar Pakistan na cikin kasashen duniya da ake ganin farmakin yan taliban na barazana matuka kan zaman lahiyar kasar.A halin yanzu kasar na cigaba da samun koma baya wajen gwagwormayar da ta dokufa da yan kungiyar taliban.Praministan kasar Britaniya David Cameron ya furuta cewa, kasar na kawo goyon baya ga aikin ta’adancin.Ya jadada cewa babu maganar da -na -sani kan wanan furuci na cewa Pakistan na goyama yan kungiyar taliban baya.A yau ne ake sa ran zuwan shugaban kasar Pakistan Asif Ali Zardari a kasar Britaniya a wata ziyara ta kwanaki 5 da zai gudanar.A na sa ran wanan ziyara za ta kawo haske a kan kwankwonton da kasar Britaniya ke da shi kan kasar Pakistan wajen goyon bayan yan Taliban ko kuma yan ta’ada baki daya.Wasu yan kasar ta Pakistan su na ganin lamarin ziyarar shugaban kasar tamkar rashin fusa’a ,sabili da yaddaa lamura su ka kassance a cikin kasar a yanzu haka.Ambaliyar ruwa ,mace-mace da tashin hankulla barkatai.