Isa ga babban shafi
Majalisar Dinkin Duniya - Pakistan

Majalisar Dinkin Duniya ta kaddamar da gidauniyar Pakistan

kasar Pakistan
kasar Pakistan Reuters
Zubin rubutu: Bashir Ibrahim Idris
Minti 1

MAJALISAR Dinkin Duniya, ta kaddamar da gidauniyar agajin Dala miliyan 460 dan taimakawa kasar Pakistan.Yayin da yake bayani kan irin ta’adin da ambaliyar ruwar tayi, Jakadan Pakistan a Amurka, Abdullah Hussein Haroon, yace ambaliyar ta wanke kauyuka 4, 772.Jakadan yayi Karin bayani kan halin da ake ciki, inda yake cewa, a halin yanzu sun yi asarar kauyuka 4,772 a Yankunan uku da ruwan yayi ta’adi, kauyuka 15,000 daga Punjab, 468 a Hydra Pakturukwa, 2600 a Buluchistan, shi yasa a halin yanzu babu san adadin wadanda suka rasa rayukansu ba. Babban jami’in hukumar Jin kai ta Majalisar, John Holmes, yace basu taba ganin irin matsalar da Pakistan ta samu kanta a ciki ba, inda ya zama wajibi kasashen duniya su taimakawa kasar, ganin yadda rashin abinci da muhalli ke barazana wa miliyoyin jama’a. 

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.