Isa ga babban shafi
Pakistan

Kayan Agaji Na Kudi Dala Miliyan 227 Sun Fara Zuwa Pakistan

Halinda mutane ke ciki a kasar Pakistan
Halinda mutane ke ciki a kasar Pakistan rfi
Zubin rubutu: Garba Aliyu
Minti 2

A Kasar Pakistan, an fara samun kayayyakin agaji daga kasashen duniya, sakamakon mummunar ambaliyar ruwan sama data shafi mutane akalla miliyan 20.Asusun da Majalisar Dinkin Duniya ta budedomin tallafawa mabukata sun sami kayan agaji na kudin Amirka Dala Miliyan 227.8, kwatan kwacin rabin yawan kudaden agajin da Majalisar Dinkin Duniya tace tana bukata. Mai magana da yawun majalisar Uwargida Elizabeth Byrs tace akwai shaawa yadda aka fara bada agaji, amma kuma akwai bukatar ganin an gaggauta kai kayan agaji kasar saboda dimbin mabukata dake jiran ganin sun sami tallafi.Ambaliyar wadda ba'a taba ganin mummuna irinta ba, tasa mutane da dama rasa muhallansu da dukkan kayan abinci, yayinda mutane akalla 1,600 ne suka rasa rayukan su.A wani sansani dake gunduman Punjab, akwai mutane akalla 3,000 wadanda ke zaune cikin wani kazamin yanayi, babu abinci gashi sauro nata cizonsu.Kasashen duniya da dama sunyi alkawarin bada agajin makudan kudade domin tallafawa mutanen da suka tagayyara.  

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.