Mamata Na Karuwa A Pakistan
Wallafawa ranar:
Jami'an aikin agaji a kasar Pakistan sunce yawan mamata nata karuwa sakamakon ambaliyar ruwan sama dan tsakanin nan, domin mamatan sun haura 1,600.Wannan mummunar ambaliyar ruwan-sama dai da ba'a taba ganin irinta ba, tasa mutane samada miliyan 17 cikin wani hali, yayinda mutane akalla miliyan takwas basu da abinci da zasu ci.Jami'ai sunce yawan mamatan na iya karuwa, domin ba'a kammala dukkan kididdiga ba tukuna.Alkaluman mamatan ya zuwa yanzu na nuna cewa mamata 1,086 sun rasa rayukansu ne a yankin Arewa maso yammacin Khyber Pakhtunkhwa, 183 a yankin Arewacin Gilgit-Baltistan, 109 a yankin kudancin Sindh, 103 a tsakiyar Punjab, 71 a yankin Kashmir sai kuma 48 a yankin kudu maso yammacin Baluchistan.