Duniya

Assussun bada lamani na duniya,da cacar baki kan karfin kudi

Dominique Strauss-Kahn,babban darakatan assussun bada lamani na duniya
Dominique Strauss-Kahn,babban darakatan assussun bada lamani na duniya REUTERS/Larry Downing

Shugaban hukumar kula da bada Lamuni ta Duniya Donimique Strauss-Kahn ya bayyana cewa cece kucen da ake yi kan karfi kudi tsakanin manyan kasashe duniya, ya na janyo komabaya ga farfadowar tattalin arzikin duniya. Daya daga cikin alamun shi ne yadda wasu kasashe ke zargin wasu na cewa ana tsara yadda karfin kudin zai kasance domin samun garabasa. Wannan yaki game da kudi ba zai kawo wata riba ga duniya , abunda muke bukata karin hadi kai.