Philippines

Ambaliyar ruwa ta Hallaka Mutane 10

Philippines inda aka samu ambaliyar ruwa
Philippines inda aka samu ambaliyar ruwa Ảnh: Reuters

Wata Mummunar guguwa mai dauke da ruwan sama a kasar Philippines, ta hallaka akalla mutane 10, tare da lalata gonakin shinkafa da masara, abinda zai tilastawa kasar sayen abinci daga kasashen waje.Maura Lizarondo, mataimakin Daraktan dake kula da aiyukan noma a kasar, ya ce gonaki da dama sun lalace sakamakon guguwar. Hukumomi sun bayyana cewa dadin asarar da guguwar ta haifar cikin yankin arewacin kasar ta Philippines zai iya zarce yadda aka kiyesce, saboda katsewar layukan sadarwa da aka samu, abunda ya janyo sai daga bisani za a iya tantance hakikanin abunda ya faru.Yanzu haka wannan guguwa mai karfin gaske ta nausa zuwa yankin kasar China. Wata guguwar mai dauke da ruwan sama data ratsa Vietnam ta hallaka akalla mutane 31 tare da haifar da ambaliyar ruwa, yayin da wasu mutanen fiye da 20 suka bace.