Koriya ta Kudu

Korea ta Kudu Tayi Barazanar Maida Martani

Harin farko tsubirin Yeonpyeong na korea ta Kudu bayan harin Korea ta Arewa
Harin farko tsubirin Yeonpyeong na korea ta Kudu bayan harin Korea ta Arewa rfi

Kasar Korea ta Kudu tayi barzanar maida kazamin martani muddin dai Korea ta Arewa tayi gigin sake kai mata hari ta sama kamar yadda tayi kwanan baya.Sabon Ministan Tsaro na Korea ta Kudu, Kim Kwan-jin ne ya fadi haka yau.Wadannan kalaman na zuwa ne bayan wani atasayen soja da Dakarun Amirka dana Japan suka kammala a yankin ruwan Korea.Ya fadi cewa shakka babu korea ta kudu zata maida martani mara kyau ta sama muddin dai aka sake kai mata hari ta sama.