Abu Dhabi
An Kama Mutun da Macizai A Jirgin Sama
Wallafawa ranar:
Wani mutumin kasar Saudiyya dake dauke da macizai da aku cikin jirgin sama daya tashi daga Jakarta an kama shi a filin Jiragen Sama na Abu Dhabi.Mutumin na shirin shiga wani jirgin sama ne lokacin da wani ma'aikacin jirgin ya hango kunshi na motsi hannun mutumin, nan da nan aka kama shi.Ma'aikatan jirgin sun bukaci mutumin daya koma gefe domin a duba kunshin inda aka ga macizai hudu da Aku biyu.Babban jami'in Tsaro dake filin jiragen sama na Abu Dhabi Khamis al-Marar ya fadi cewa katon laifi ne daukan dabba cikin jirgin sama ba tare da izini ba.