Iraki

Majalisar Dinkin Duniya Ta Amince Iraki Tayi Aikin Nukiliya

Mataimakin Shugaban kasar Amirka Joe Biden da Ministan Waje na Iraki Hoshyar Zebari kafin taro na yau
Mataimakin Shugaban kasar Amirka Joe Biden da Ministan Waje na Iraki Hoshyar Zebari kafin taro na yau rfi

Majalisar Tsari ta Majalisar Dinkin Duniya ta bada amincewar ta ga kasar Iraki data cigaba da aikin ta na samar da Nukiliya , al’amarin da ke kawo karshen takunkumi da aka malkaya wa kasar Irakin  shekaru 19 da suka gabata.Kudurori uku ne suka kaiga karshen takunkumin da aka malkayawa wannan kasa mai arzikin man fetur wadda akayi raga raga da ita zamanin marigayi Shugaban kasar Saddam Hussein.Na farko kudurin ya nemi dage takunkumin da aka malkayawa Irakin cikin shekara ta 1991 dake hana ta aikin Nukiliya.Kudiri na biyu shine dage takunkumin da aka sanya domin Marigayi Saddam Hussein ya yi amfani da kudaden kasar na Man fetur domin sayen abinci da magunguna domin mutanen kasar ta Iraki.Kudiri na uku ya nemi majalisar Dinkin Duniya data kara wa'adin ta da watanni shida domin asusun raya kasar Iraki na miliyoyin kudade wanda aka kaddamar cikin shekara ta 2003 saboda sarrafa kudaden albarkatun man fetur da sauran kudaden shiga da kasar ke samu.