Afghanistan

Bam da aka dasa fegen hanya ya hallaka mutane 14 a Afghanistan

Hare hare kunar bakin wajen Afghanistan
Hare hare kunar bakin wajen Afghanistan REUTERS

Fashewar wani Bam da aka dana a gefen titi, ya yi, sanadiyar mutuwar mutane 14, 'yan gida guda, dake tafiya a cikin wata motar safa, a yankin Herat na yammacin kasar Afghanistan, kamar yadda kakakin hukumomin yankin, Rafi Behrozyan ya sanar.Sai dai kuma majiyar bata bayyana ko mutane nawa ke cikin motar ba dake daukar mutane 20.A gefe guda kuma, ofishin ministan tsaron kasar Afghanistan ya bayyana cewa, wani harin jiragen saman da Rundunar tsaro ta NATO ko OTAN da ta kai a jiya Laraba, a yankin kudancin kasar ta Afghanistan, ya yi sanadiyar mutuwar dakarun gwamnatin kasar hudu, inda ofishin ministan ya ce, ya fara bincike kan faruwar lamarin.