China-Indiya

Kasashen China da Indiya zasu bunkasa harkokin kasuwanci

Prime Ministan China Wen Jiabao da takwaransa na Indiya Manmohan Singh a birnin New Delhi.
Prime Ministan China Wen Jiabao da takwaransa na Indiya Manmohan Singh a birnin New Delhi. REUTERS/B Mathur

Kasashen China da Indiya sun saka hanu kan yarjejeniyar bunkasa huldar kasuwanci tsakaninsu ta dalar Amurka bilyan 100 nan da shekaru biyar masu zuwa.Prime Ministan Indiya Manmohan Singh da takwaransa na China Wen Jiaboa, suka amince da yarjejeniyar kasuwanci zuwa shekara ta 2015, a birnin New Delhi na kasar ta Indiya.A takardar bayan taro da shugabannin biyu suka bitar, ta bayyana amince da kara yawan kayan da Indiya zata fitar zuwa kasar China.Kasashen biyu na China da Indiya suke kan gaba wajen yawan mutane da karfi tattalin arziki tsakanin kasashen nahiyar Asia, kuma mahukuntan birnin Beijing sun kokawa bisa mafakar siyasa da Indiya ta baiwa shugaban addinin Tibet Dalai Lama, wanda yake kasar tun bayana boren da sukayi wa China cikin shekarar 1959.