Isra'ila-Palasdinawa

Gabas ta tsakiya :Gwamnatin Israila ta Haramta hulda da ta Palestinu.

Shugaban diplomasiyar kasar Israila Avigdor Lieberman, tare da manzon Amurika a gabas ta tsakiya George Mitchell
Shugaban diplomasiyar kasar Israila Avigdor Lieberman, tare da manzon Amurika a gabas ta tsakiya George Mitchell ( Photo : Reuters )

Ministan Harkokin wajen Isra’ila, Avidgor Liberman, ya bukaci kasar Isra’ila da ta kaucewa sanya hannu a kan duk wata yarjejeniya da Gwamnatin Palasdinawa, gwamnatin da ya danganta da haramtaciyar gwamnati.Ministan wanda ke ganawa da Jakadun Isra’ila a kasashen duniya, ya ce ya haramtama Isra’ila ta amince da duk wata yarjejeniya da wannan Gwamnati, domin ba ta samun goyan bayan daukacin Palasdinawa.