Taiwan

Masu cin kare an ci su tarar kudi dala 3,000 a Taiwan

dabbar kare
dabbar kare

An ci tarar Wasu ‘yan kasar Taiwan guda biyar kudi dalar Amurka 3,000 da aka kama da laifin cin dabbar kare guda biyu abinda aka bayyana irinsa na farko a yankin Taipei.Mutanen guda bayar wadanda dukkaninsu sun haura shekaru 50, an kama su ne lokacin da suke yanka kare a wani dajin Yingke da ke wajen Taipei wanda hakan kuma laifi ne a kasar kan cin zarafin dabbobi.Duk da cewa wasu daga kasar China a kasar sukan ci kare, amma a tsarin dokar kasar laifi ne mutum ya ci kare ko mage kuma duk wanda aka kama a kan ci shi tarar kudin kasar dala 500,000 a tsarin dokar kasar.