Iraqi

Wani harin Bom ya kashe sojojin Amurka 2 a Iraqi

Taswirar Iraki
Taswirar Iraki rfi

Wani bom da ruwan albarussai sun yi sanadiyar mutuwar sojojin Amurka uku da wasu fararen hular kasar Iraqi tare da raunana mutane sama da Ashirin, kamar yadda jami’an tsaron kasar Iraqi suka sanar.Wani jami’in tsaron kasar yace a safiyar yau ne bom ya tashi a wata mota a harabar wani ofishin ‘yan sanda a Baquba da ke arewa da babban birnin kasar. Bayan tashin bom din ne kuma aka ci gaba da harba gurneti a ofishin ‘yan sandan.A cewar likita Firas Al-Dulani da ke aiki da babbar asibitin Baquba ya bayyana cewa yara mata ‘yan makaranta 10 ne suka ji rauni da wasu maza guda biyu sai kuma ‘yan sanda 8 da suke a ayanzu haka cikin mawuyacin hali.Da safiyar yau ne kuma wani jami’in ma’aikatar harakokin cikin gidan kasar, ya bada sanarwar mutuwar wata mata kirista mai suna Rafah Toma da wasu ‘yan bindiga suka budewa wuta.A makon daya gabata dai mabiya addinin kirista a kalla mutane biyu ne suka mutu mutane 16 suka ji rauni sanadiyar wani hari da aka kaiwa kirista a birnin Bagadaza. A wani harin kuma da aka kai wata Coci a watan Octoban bara, harin ya yi sanadiyar mutawar mutane sama da 40.