Japan-Koriya ta Kudu

Koriya ta kudu da Japan zasu kulla amintaka kan sha’anin tsaro

Shugaban kasar Japan Naoto Kan
Shugaban kasar Japan Naoto Kan Reuters

Gwamnatocin kasashen Koriya ta kudu da Japan sun amince su tattauna da juna domin farfado da dangantakar kasashen biyu tun bayan mulkin mallakar kasar Japan a yankin Koriya wanda ya kawo karshe a shekarar 1945. Wannan dai na zuwa ne bayan da ministan tsaron kasar Koriya Kim Kwan-Jin ya cimma matsaya da takwaransa na kasar Japan Toshimi Kitazawa kan sasanta kasashen biyu musamman ga harin da koriya ta Arewa ta kai wa koriya ta kudu a watan Nuwamban bara. Mnistocin tsaron kasashen biyu sun ce harin da kasar Koriya ta Arewa ta kai a tsibirin Yeonpyeong da kuma furucin kasar kan makamashin Uranium wani al’amari ne da ba zasu amince da shi ba. Wanda hakan ya sanya ministocin biyu suka amince da yarjejeniyar musayar soji a asirce domin samar da zaman lafiya tsakanin kasashen.Ana dai sa ran nan ba da jimawa bane Prime Ministan kasar Japan Naoto Kan da takwaransa na Koriya ta Kudu Lee Myung-Bak zasu tattauna da juna don amincewa da yarjejeniyar.