Yemen

Shugaban Yemen Na Zargin Amirka Da Israela

Masu zanga zanga a kasar Yemen
Masu zanga zanga a kasar Yemen rfi

Shugaban  Kasar Yemen, Ali Abdallah Saleh, ya zargi Amurka da Isra’ila, da yunkurin kifar da Gwamnatin sa, yayin da dubban mutane ke cigaba da zanga zanga a cikin kasar.Shugaba Saleh yayi zargin cewar, an kitsa zanga zangar da akeyi a kasashen larabawa ne daga Israila da Amurka, dan kauda shugabanin su.