Pakistan

Harin kunar bakin wake ya hallaka mutane akalla 20

Akalla mutane 20 sun hallaka yayin harin bam, sannan wasu fiye 120 suka samu raunika, lokacin da wata mota dauke da bam ta tarwatse.Fashewar butun iskar gas a wannan yankin ya janyo motoci da gine gine masu yawa kamawa da wuta.Yan sanda sun bayyana cewa yawan wadanda suka hallaka zai haura, sakamakon raunikan da mutane masu yawa suka samu. Kasar ta Pakistan tana fuskan hare hare daga kungiyoyin tsageru masu dauke da makamai, wadanda suka hana kasar sakat.