Bangladesh

Kotun kasar Bangladesh ta tabbatar da sallam Yunus daga bakin aiki

Mohammad Yunus masanin tattalin arziki da fara kafa bankin taimakawa al'uma
Mohammad Yunus masanin tattalin arziki da fara kafa bankin taimakawa al'uma Reuters/Andrew Biraj

Wata kotun kasar Bangladesh ta tabbatar da sallamar da hukumomin kasar suka yiwa Mohammad Yunus daga bankin Grameen, wanda ya kafa.Tunda fari Yunus Farfasa kan fannin tattalin arziki ya kalubalanci matakin babban bakin kasar na cire daga mukamun shugaban wannan banki na Grameen, saboda dalilan wuce shekarun ritaya da ya yi yana aiki, tare da cewa haka siyasa ce kawai.Mohammad Yunus ya taba samun lambar kyauta ta Nobel, saboda aikin da ya yi na kirkiro banki taimaka wa al’umma farkon shekarun 1980, abun da zama wanda duniya ke koyi da shi, domin kawar da talauci musamman a kasashe ‘yan rabbana ka wadata mu.