Malaysia

Kotun Malaysia ta yi watsi da zargi luwadi kan madugun 'yan adawa

Anwar Ibrahim madugun 'yan adawan kasar Malaysia
Anwar Ibrahim madugun 'yan adawan kasar Malaysia Photo: Reuters

Wata Kotu a kasar Malaysia, dake shari’ar zargin luwadi da akewa shugaban 'yan adawa, Anwar Ibrahim, taki amincewa da shaidar gwajin jinin da aka masa.Alkalin kotun, Zabidin Mohammed Diah, ya ce ba zai amince da shaidar ba, saboda an dauki jinin ne ta hanyar da bata kamata ba, lokacin da aka tsare wanda ake zargin.