Manya-manyan masu kudin duniya kamar yadda mujalasar Forbes ta jerasu
Wallafawa ranar:
Jaridar ta ruwaito cewar, Carlos Slim, Dan kasar Mexico ke matsayi na daya, ganin yadda dukiyarsa ta samu habakar sama da Dala biliyan 20 daga bara zuwa bana,inda yanzu haka yake da Dala biliyan 74, yayin da Bill Gates yake matsayi na biyu da Dala biliyan 56.Warren Buffet, Dan kasar Amurka ke matsayi na uku, da Dala biliyan 50, sai kuma Bernard Arnault, Dan kasar Faransa a matsayi na hudu da Dala biliyan 41.Larry Ellison, da kasar Amurka ke matsayi na biyar, Lakshmi Mittal, Daga kasar India a matsayi na shida, da kuma Amancio Ortega, daga Spain amatsayi na bakwai, da Dala biliyan 39, 31 da kuma 31 bi da bi.Lilian Betancourt, Yar kasar Faransa, wanda ake zargi da kaucewa biyan haraji, da kuma baiwa Jam’iyar Sarkozy taimako, ke matsayi na 15, da Dala biliyan 23.Roman Abramovic, mai kungiyar kwalon kafar Chlsea ke matsayi na 50, da Dala biliyan 11, Prime Ministan Italy, Silvio Berlusconi ke matsayi na 74, da Dala biliyan 9, Alisher Usmanovic, mai arsenal ke matsayi na 100 da Dala biliyan 7,A cikin hamshakan attajiran dai 200, babu wani daga nahiyar Afrika.