Japan

Mutane 56 sun hallaka bisa girgizar kasar Japan

Girgizar kasar Japan ta Tsunami
Girgizar kasar Japan ta Tsunami REUTERS/NHK via Reuters TV

Wata karfarfar girgizar kasa mai karfi maki 8.9 ta ritsa da kasar Japan, inda akalla mutane 56 sun hallaka, bisa wannan dake zama mafi mufi da kasar ta fuskanta cikin shekaru 140. Wannan girgizar kasa ta Tsunami da ta afka wa arewa maso gabashin Japan, ta share motoci, jiragen ruwa da gijane, kamar yadda tashar telebijin kasar ta kasar ta nuna.Girgizar kasar ta janyo tashin wuta har zuwa Tokyo babban birnin kasar, wanda ake jin tsoro mutane masu yawa sun hallaka.Girgizar kasa ta faru a waje mai nisan kilo mita 400 daga babban birnin kasar, a karkashin teku, kuma anji motsinta a birnin Beijing na kasar China. Tuni hukumomin kasashen Philippines, Indonesia, Taiwan da wasu kasashen tekun Pacific suka bada gargadin yuwuwar samun Tsunami.