Japan

Fiye da mutane 1,300 sun hallaka sakamakon girgizar kasar Japan

Yomiuri / Reuters

An fara gudanar da aiyukan agaji bayana girgizar kasar Japan ta Tsunami data hallaka daruruwan rayuka mutane, tare da share kauyuka masu yawa.Yan sandan kasar sun bayyana cewa fiye da mutane dubu 215 ke samun mafaka cikin yankin arewa maso gabashin kasar da aka samu bala’in.Gwamnatin kasar ta Japan ta ce ya yi wuri a tantance hakikanin ta’adin da girgizar kasar ta haifar, amma akwai yuwuwar mutanen da suka hallaka zasu kai 1,300.Motsin girgizar kasar mai karfi maki 8.9 ya kai yankuna masu nisa na tekun Pacific. Mahukuntan kasar sun yi gargadin yuwuwar samun yoyo daga tashar Nukiliya ta kasar, wadda ake kokarin tabbatar da cewa babu abunda ya same ta.