China

Gwamnatin China ta bayyana shirin kaddamar da sauye sauyen siyasa

Wen Jia Bao Prime Ministan kasar China
Wen Jia Bao Prime Ministan kasar China

Prime Ministan kaasr China, Wen Jibao, ya ce dole China ta aiwatar da sauye sauyen siyasa, domin tafiya dai dai da zamani.Yayin da yake ganawa da manema labarai, Wen Jibao ya ce, muddin ba’a samu sauyin siyasa ba, ba za’a samu nasarar sauye sauyen tattalin arziki ba. Wannan daidai lokacin da guguwar siyasa ke ci gaba da kadawa cikin kasashen Larabawa na neman samun demokaradiya.