Afghanistan

Mutane 33 sun hallaka sanadiyar harin kunar bakin waken Afghanistan

Mutane 33 sun hallaka cikin ahrin kunar bakin waken da akakai inda ake diban sabbin sojaji, a yankin arewacin kasar Afghanistan.Harin na yau Litinin ya kuma jikata mutane fiye da 40 kamar yadda jami’ai suka tabbatar. Kawo yanzu babu mutun ko kungiyar da ta dauki alhakin kai wannan hari. Akwia dubban dakarun kasashen duniya masu aikin tabbatar da zaman lafiya a kasar ta Afghanistan, tun bayan kutsen da Amurka ta jagoranta a shekara ta 2001, wanda ya kai ga kifar da gwamnatin Taliban daga madafun iko.

AFP/Massoud Hossaini