Japan

Fiye da mutane 2400 sun hallaka sakamakon girgizar kasa ta Japan

An Sake samun wasu fashe fashe a tashoshin nukiliyar kasar Japan, abinda ya haifar da gobara, da kuma barazanar tsiyayar iska mai guba.Prime Ministan kasar Naoto Kan, ya tabbatar da barazanar, inda ya bukaci mutanen dake zama kilo mita 30 daga tashoshin da su zauna cikin gidajensu, yayin da aka tabbatar da mutuwar mutane 2,414 yanzu haka.