Chadi

Kasar Chadi ta baiwa Chian kwangilar gina layin dogo

Idriss Déby shugaban kasar Chadi
Idriss Déby shugaban kasar Chadi © Marion Urban/RFI

China ta samu nasarar aikin kwangilar gina hanyar jirgin kasa a kasar Chadi, wanda zai ci Dala biliyan bakwai.Ministan samar da kayan more rayuwa, Adoum Younousmi, ya ce shekara mai zuwa ta 2012 za’a fara aikin, wanda zai ci tsawon kili mita 1,344, kuma zai hada kasar da kasashen Sudan da Kameru.