Japan

Tashar Nukiyar kasar Japan ta na fuskantar barazana

REUTERS/Kyodo

Hadarin Nukliyar a cibiyar Fukushima ta kasar Japan ya kai kololuwar muninsa da kashi 6 a cikin 7 bisa ma’aunin duniya ta hanyar yada sanadarai masu guba a cikin jama’a, kamar yadda shugaban hukumar kula da tsaron nukliyar kasar Faransa ASN Andre Claude Lacoste ya sanar.Shi kuma shugaban hukumar dake kula da hasashen yanayi ta duniya OMM cewa ya yi iska ya kada daga barin yankin dake fuskantar barazana na kasar japan da kuma na kasashen duniya.Inda yak ara da cewa duk da cewa matsayin Barazarar ya kai 6 bisa 7 al’amarin ya canza ba kamar jiya ba. Wanann kuma yana tafiya ne bisa gudummuwar da mahukumtan nukliyar kasar fransa ke badawa ne.Masu aikin agaji a kasar ta Japan, sun yi nasarar ceto wasu mutane biyu da ransu, bayan sun kwashe kwanaki hudu a karkashin gine ginen da suka rushe.Cikin wadanda aka ceto, kamar yadda Gwamnatin kasar ta sanar, harda wata mata mai shekaru 70, kuma ance bata fuskantar wani hadari. Rohotanni sun nuna cewa akwai akalla mutane 10,000 sun hallaka sakamakon girgizar kasar.