Japan

Mutane 15,000 Suka Mutu Ko Suka Bace a Japan

Jiragen Saman sojin kasar Japan, na cigaba da zuba ruwa kan tashar nukiliyar kasar, ta Fukushima, dan ganin an sanyaya ta, domin a magance tiririn dake fita daga ciki.Ministan Tsaron kasar, Toshimi Kitazawa, yace baicin jiragen saman, za’a tura motocin soji 11 dan taimakawa aikin.Yan Sanda sun ce, ya zuwa yanzu mutane 15,000 aka tabatar da mutuwarsu, a girgizar kasa, da kuma igiyar ruwan Tsunami, da ta abkawa kasar.A halin da ake ciki, Sarkin sarakunan kasar yayiwa al’umar kasarsa da suka fada cikin mawuyacin halin barazanar Nukliya jawabi, inda sama da mutane dubu 500 ke bukatar taimako sakamakon Ambaliyar Ruwan tsunami da girgizar kasar ta haddasa.A cikin wani jawabi na yan mintina da ya yi ta kafar TV din kasar Sarki Akihito ya yi ya bayyana cewa suna iya hana ci gaba da gurbacewar.A karo na farko dai ke nan sarki Akihito ya yi jawabi ga yan kasar ta Japon tun bayan wanda yayi masu a 1989.  

Sojan kasar Japan na kwashe gawan wasu mamata da suka gani
Sojan kasar Japan na kwashe gawan wasu mamata da suka gani rfi