Japan

Ana kokarin sanyaya makamashin Nukiliyar kasar Japan

Sojojin kasar Japan dauke da gawawwakin wadanda suka mutu a kauyukana da girgizan kasar ta shafa
Sojojin kasar Japan dauke da gawawwakin wadanda suka mutu a kauyukana da girgizan kasar ta shafa Reuters

Mahukuntan kasar Japan na shirin sake komawa aikin sanyaya makamashin Nukiliyar kasar, domin kaucewa abunda zai iya zama mummunan bala’i. kimanin jirage hudu ne masu saukar Angulu ke dauke da ton ton na ruwa domin magance matsalar da ta afkawa makamashin da suka tarwatse sanadiyar mummunar girgizar kasar da ta auku a kasar.Ana yunkurin tabbatar da cewa babu tsiyaya da aka samu a tashar nukiliyar da ke Fukushima mai nisan kilo mita 250 arewa maso gabashin Tokyo babban birnin kasar.Hukumomin kasar ta Japan sun tabbatar da mutuwar mutane 5,600, yayin da wasu 9,500 suka bace bayan girgizar kasa mai karfin maki 9 data auku a kasar ta Japan ranar Jumma’a data gabata. Kuma girgizanr kasar na kokarin jefa kasar cikin sabon bala’in yuwuwar samun tsiyayan makamashin nukiliya.