Japan

Ana ci gaba da neman shawo kan matsalar Nukiyar Japan

Injiniyoyin tashar nukiyar kasar Japan na ci gaba da aikin sanyaya makamashin nukiyar kasar, bayan girgizar kasa data hallaka dubban mutane.Hukumomin sun tabbatar da mutuwa tare da bacewar mutane 18,000, bayan gano gawauwaki 7,200 a buraguzan gine gine.Tunda fari hukumomin kasar ta Japan sun dauki rikicin nukiyar tashar Fukushima a matsyain wani karamin lamari, amma yanzu ankai shi mataki na biyar cikin matakai bakwai na auna balai da kasashen duniya ke anfani da shi.MDD ta ce lokaci na kure wa Japan wajen daidaita lamura a tashar ta nukiya. 

Reuters