Fiye da mutane 15,000 sun hallaka a girgizar kasar Japan
Kasar Japan tana samun nasara kan aikin da takeyi na kare samun matsalar yoyon makamashin nukiya, yayin ake gab da mayar da wuyar lantarki.Hukumomin kasar sun tabbatar da mutuwar fiye da mutane 15,000 bayan girgizar kasa da Tsunami da suka daidaita, wadda take sahun gaba cikin kasashen masu karfin tattalin arziki.Akwai kimanin injiniyoyi 300 masu aikin sake daidaita aiyukan nukiyar kasar ta Japan a tashar Fukushima, abunda ke neman zata balai mafi muni da duniya zata gani kan nukiya tun bayan na Chernobyl shekaru 25 da suka gabata.Kiyasi na nuna cewa kasar ta Japan tana bukatar kudaden da suka dala bilyan 200 domin sake gina ta’adin da girgizar kasar ta yi.
Wallafawa ranar: