Japan
Makamashin Nukiyar Japan ya gurbata ruwan sha
Wallafawa ranar:
Hukumomin Kasar Japan, sun ce sun gano cewar iskar dake fita daga cikin tashoshin nukiliyar kasar, sun gurbata ruwa famfon birnin Tokyo, kuma shan ruwan zai yi illa ga kananan yara.Jami’an birnin, sun bukaci iyayen yara, da su kaucewa baiwa yaransu ruwan famfo, saboda hadarin dake ciki.