Japan

Mutane 25,000 sun hallaka ko sun bace bayan girgizar kasa

Reuters/Damir Sagolj

Fiye da mutane 25,000 sun hallaka ko kuma sun bace sanadiyar girgizar kasar da aka samu a kasar Japan.Hukomin kasar suka tabbatar da haka kwanaki 12 bayan faruwar girgizar kasar data haifar da igiyar ruwa na Tsunami a yankin arewa maso gabashin kasar.Rindinar ‘yan sandan kasar tabbatar da samun gawauwaki fiye da 9000. Sannan an tabbatar da cewa mutane 2,755 sun samu raunika.Akwai dubban mutane da girgizar kasar ta daidaita, bayan awaun gaba da gidajensu.Girgizar kasar ta zama mafi muni da kasar ta Japan ta fuskanta bayan wadda ta ritsa da ita a shekarar 1923, da ta yi sanadiyar mutuwar mutane 142,000. A wani labarin hukumomin kasar ta Japan, sun gargadi 'yan kasar da su kaucewa baiwa kanana yara ruwan famfo, saboda gurbacewar sa da iskar dake fita daga tashar nukiliyar kasar.Wannan umurni ya dada jefa kasar cikin rudani, ganin yadda matsalar fitar iskar ta harbi anfani gonan da Japan ke fita da shi zuwa kasashen waje, abinda ya sa Gwamnati ta dauki matakin hana fita da kayan abinci daga yankin.Wani jami’in Gwamnatin Japan, ya ce ya zuwa yanzu an samu kashi 210 na adadin iskar dake fita daga tashar nukiliyar Fukushima, a cikin ruwan garin, wanda ya zarce ka’idar da zai iya yin illa ga Bil Adama.Tuni kasar Amurka ta haramta shiga da madarar da akeyi daga Japan, yayin da kasar Faransa ta bukaci kungiyar kasashen Turai, da ta sanya shinge kan kayan da ake kaiwa nahiyar daga Japan.Prime Ministan kasar Japan, Naoto Kan, ya haramta fitar da kayan abinci irinsu madara, da kayan lambu zuwa kasahsen waje, daga Yankin da aka samu hadarin.