Japan

Ma’aikatan tashar Nukiliyar Japan uku sun kamu da cuta

Reuters

Mahukuntan kasar Japan, sun sanar da kamuwar wasu ma’aikata guda uku da tururin iskar Nukiliya mai guba daga cikin ma’aikatan dake aiki a tashar nukiliyar Fukushima. A daidai lokacin da kasashen duniya ke haramta shigo da kayan abincin da kasar Japan ke samarwa.Sai dai kuma gwamnatin kasar ta bada umurnin ga al’ummar kasar cewa, yanzu yara kananan na iya shan ruwan famfo, saboda rashin hadarin dake ciki.Kasar Australiya da Canada da Hong kong da kasar Amurka na daga cikin kasashen Duniya da suka dauki matakin haramta amfani da kayayyakin kasar Japan kamar yadda kasar Faransa ke kokarin kungiyar tarayyar kasashen Turai ta amince da wannan matakin.