Yemen

Gangamin masu adawa da masu kaunar Saleh a Yemen

daruruwan masu zanga-zangar kin jinin gwamnatin Abdalla Sale a wajen harabar Jami'ar Sanaa
daruruwan masu zanga-zangar kin jinin gwamnatin Abdalla Sale a wajen harabar Jami'ar Sanaa Reuters

Daruruwan ‘yan kasar Yemen ne suka fito a yau Juma’a babban birnin kasar a ci gaba da nuna kyamar gwamnatin shugaban kasar Ali Abdallah Saleh a daidai lokacin da masu kaunarsa ke amsa kiransa lokacin da zai gabatar da jawabi ga ‘yan kasar.Masu kaunar shugaban sun yi dandazo ne a daidai harabar jami’ar Sanaa domin sauraren jawabin shugaban. Sai dai kuma jami’an tsaron kasar suna gudanar da kwakkwaran bincike ga mutanen da ke kokarin shiga harabar Jami’ar don gudun kawo wani tarnaki ga taron.A lokacin da shugaban yake jawabi ga masoyansa ya sha alwashin tsayawa tsayin daka domin ganin ya yaki masu adawa da gwamnatinsa. Shugaban ya kuma ce gwamnatinsa zata ci gaba da kokarin tabbatar da tsaro da ‘yanci da dorewar kasar yemen ta kowace hanya.A ranar larabar da ta gabata ne majalisar kasar ta amince da dokar ta baci da shugaban ya bukata bayan zubar da jinin da ya faru a kasar. sai dai kuma masu zanga-zangar adawa da shugaban sun bayyana gudanar da wata kazamar zanga-zanga a 1 ga watan Aprilu a fadar shugaban kasar al’amarin da wasu ke shakkun zai haifar da rasa rayuka da dama.