Isra'ila

Isra’ila ta shirya daukar Fansa, inji Netanyahu

Prime Ministan Israi'la Benjamin Netanyahu.
Prime Ministan Israi'la Benjamin Netanyahu. REUTERS/Ariel Schalit

Prime Ministan kasar Israila Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa kasarsa a shirye take da karfin tuwo domin daukar Fansa ga hare haren da dakarun yankin Gaza suka kai wa kasarsa da kuma harin wani Bom da aka kai a Jerusalem.A daidai lokacin da zai gana da Robert Gates na Amurka, Netanyahu ya bayyana wa manema labarai cewa Israila na fama da hare hare kuma a shirye take ta kawo karshen hare haren.A yanzu haka dai Amurka ta goyi bayan matakin Isra’ila na mayar da hare hare kamar yadda Robert Gates Sakataren harakokin tsaron Amurka ya shaidawa manema labarai. Sai dai kuma Mista Gates ya bukaci shugabannin Israila da Palasdinawa wajen daukar mataki domin tabbatar da zaman lafiya a tsakaninsu.