Syria

Syria zata yi watsi da dokar ta baci

Masu Zanga-zanga lokacin da suka yi wani gangami kusa da Masallacin Omari a birnin Dar'a
Masu Zanga-zanga lokacin da suka yi wani gangami kusa da Masallacin Omari a birnin Dar'a Reuters

Gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad ta kasar Syria ta bayyana shirin watsi da dokar ta baci da kasar ke anfani da shi tun a shekarar 1963, tare da sakin masu rajin kare hakkin bil Adam.Masu zanga-zanga a kasar ta Syria na neman aiwatar da sauye sauyen demokaradiya, kuma fiye da mutane 50 sun hallaka yayin wani artabu da jami’an tsaro, musamman a garin Dara’a.