Japan

Mahukuntan Japan sun gano karuwar gurbataccen sinadarin makamashin nukiya

Reuters

An gano karuwar gurbataccen sinadarin makamashin nukiya a cikin ruwan dake kusa da masana’antar Nukiyar kasar Japan ta Fukushima fiye da na mako guda da ya gabata.Jami’ai sun karfafa gwiwar cewa babu illar da haka zai haifar, amma akwai damuwa kan yuwuwar ci gaba da samun tsiyayan sinadaren makamashin na Nukiya.PM kasar ta Japan Naoto Kan ya bayyana cewa babu wanda zai iya tabbatar da abun da zai faru.Girgizar kasa da igiyar ruwan Tsunami na ranar 11 ga wannan wata na Maris, sun hallaka fiye da mutane 10,000 yayin da wasu 17,000 suka bace. Akwai wasu dubban daruruwa da suka rasa gidaje.