Japan

An Kwashe Ma'aikatan Tashar Nukiyar Kasar Japan

Tashar Nukiya ta Fukushima dake kasar Japan
Tashar Nukiya ta Fukushima dake kasar Japan Reuters

Yau Lahadi, an kwashe ma’aikata daga tashar Nukiliya ta biyu dake Fukashima na kasar Japan, bayan gano karuwar turirin makamashin nukiya mai yawa, dake ci gaba da yoyewa.Mahukuntan kasar sun yi gargadin cewa akwai sauran jan aikin daidaita tashoshin nukiliyar kasar, bayan girgizar kasa da igiyar ruwan Tsunami da suka yi wa kasar kaca kaca.Fiye da mutane 27,000 sun hallaka ko kuma sun bace, sanadiyar wannan girgizar kasa ta ranar 11 ga wannan wata na Maris data afkawa kasar ta Japan, wadda take sahun gaba cikin kasashen duniya masu karfin tattalin arziki.