Syria

Shugaban Kasar Syria Na Zargin Munafukai Da Kitsa Masa Tsiya

Masu bore a kasar Syria
Masu bore a kasar Syria rfi

Shugaban kasar Syria Bashar al-Assad yayi jawabi na farko ga al’ummar kasar gameda rikicin siyasar kasar daya kaure dan tsakanin nan.Shugaban ya zargi munafukai da hannu wajen kitsa zanga zangan da aka shiga mako biyu ana yi a kasar.A jawabin da yayi ga alummar kasar kai tsaye daga Majalisar kasar,a Damascus, Shugaba Bashar al-Assad yace wannan bore na gwada karfin hadin kan mutan kasar ne.Yace yana sane da cewa al’ummar kasar na dakon jawabin nasa, koda shike babu wasu manyan sauye sauye da yayi.Shugaban ya sami kyakkyawan tarba a zauren Majalisar, inda aka rika jinjina masa a lokacin da yake gabatar da jawabin sa.