Japan-France
Shugaban Faransa Sarkozy ya isa kasar Japan
Wallafawa ranar:
Prime Ministan kasar Japan, Naoto Khan, ya ce zai rufe tashar nukiliyar Fukushima, saboda matsalolin da aka samu, wadanda ke barazana ga rayukan al’umma.Gwamnatin Japan na fama da matsalar tsiyayar iska mai guda daga tashar, tun bayan ambaliyar ruwa, da kuma igiyar Tsunami da ta shafi Yankin kasar. Shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy ya isa Tokyo babban birnin kasar ta Japan, inda ya nemi samar da wata hanyar kare hadari makamashin nukiya.