China-Faransa

Shugaban Faransa Sarkozy ya nemi daidaito kan hada hadar kudade

Shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy.
Shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy. © REUTERS

Shugaban Kasar Faransa, Nicolas Sarkozy, ya yi kiran samun daidaito wajen hada hadar kudaden duniya, inda kasuwa zata dinga daidaita farashin kudade.Yayin da ya ke jawabi wajen bude taron kasashen da suka fi habakar tattalin arzikin masana’antu ta duniya, a Nanjing, dake kasar China, shugaba Nicolas Sarkozy, ya bukaci fadada kudaden da ake anfani da su, wajen hada hadar kasuwanci , baicin kudaden Dala da Euro.Sarkozy ya ce, ya zama wajibi a samu ci gaba, wajen samun kudaden musaya a duniya, inda kasuwa zata dinga samarwa kanta matsayi, inda ya ke cewa, hakan ba zai yiwu ba, dole sai an samu dokoki na duniya, in ba haka ba, za’a samu matsala.Kasashen Yammacin duniya, na bukatar ganin kudin Yuan na China, ya samu shiga cikin kudaden da ake hada hada dasu, dan ganin an janyo kasar China ta daina rage darajar kudin ta.Shima a nashi jawabi, Sakataren Baitulmalin Amurka, Timothy Geithner, ya ce wannan matsalar banbacin kudaden musaya, shi ne ke addabar duniya yanzu haka.Mataimakin Prime Ministan China, Wang Qishan, ya yi alkawarin anfani da kasahsen duniya, dan mutunta harkokin kasuwanci a duniya.