G20

Taron Ministoci da Gwamnonin Kudi na kasashen G20 a China

REUTERS/Francois Mori

Ministocin Kudade da kuma Gwamnonin Bankunan dake kungiyar kasashen da suka fi arzikin masana’antu ta G-20, zasu gudanar da taronsu a China, inda zasu maida hankali kan darajar kudin duniya.Cikin wadanda ake saran zasu halarci taron na yau, harda shugabanin Bankin Duniya da na Hukumar Bada lamini ta duniya.