Siriya

Dokar matakan tsaro a yankin da masu adawa su ke a kasar Siriya

Jami'an tsaro a kasar Siriya
Jami'an tsaro a kasar Siriya

Dakarun kasar Siriya, sun karfafa matakan tsaro a cikin yankunan da ake ci gaba da samun masu nuna adawa ga gwamnatin kasar.Kafofin yada labaran gwamnatin sun bayyana cewa jami’an tsaro sun mayar da doka da oda.Shugaban kasar ta Siriya Bashar al-Assad ya na fuskanta matsin lamba daga kasashen duniya na neman sassauta ma masu zanga-zanga, abun da ya janyo kungiyar kasashen tarayyar Turai ta kargama takunkumi ga gwamnatin kasa.