Japan

Kasar Japan zata ci gaba da amfani da makamashin Nukiya

PM Japan Naoto Kan
PM Japan Naoto Kan Reuters/Toru Hanai

PM kasar Japan Naoto Kan ya bayyana cewa makamashin nukiya zai ci gaba da zama jigo wajen samar wa kasar makamashi.Ya kuma bayyana sake duba manufofin kasar kan yadda ake amfani da makamashin na nukiya, inda wata hukuma ta musamman zata gudanar da aikin.PM Kan ya ce an rufe tashoshin nukiyar kasar wadanda suka samu matsaloli bayan girgizar kasa da igiyan ruwa na Tsunami a watan Maris, domin bincike na musamman.