pakistan

An yi gumurzu tsakanin sojan pakistan da 'yan Al-Qaeda

REUTERS

Akalla Sojin Pakistan takwas ne suka rasa rayukansu, yayin da aka kashe Yan Taliban 10, a wani gumurzu da akayi yau da asuba, a kudancin Waziristan. Rahotannin sun ce, Yan Taliban sama da 100 dauke da muggan makamai ne suka kai hari, wajen binciken abababn hawa, inda akayi ta dauki ba dadi da jami’an tsaron.Tun bayan kasha shugaban Al-Qaeda Osama Bin Laden, ‘yan kungiyar suke ci gaba da kai hare hare ba tare da kakkautawa ba kan sojan Amurka da na kasar ta Pakistan.